Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Gasar kofin duniya 2018: Fitaccen yan wasa a gasar bana

Kylian Mbappe

Yayin da aka kammala gasar kofin duniya na wannan shekara, ga fitattun yan wasa da suka karbi lambar yabo a gasar

Gasar kofin duniya na wannan shekarar ta zao karshe inda kasara nahiyar turai, Faransa tayi nasarar lashe kofin.

Wasan ta na karshe Faransa ta doke Croatia da ci 4-2 wajen samun galabar sake daga kofin gasar bayan karo na farko a cikin shekarar 1998.

Kamar yadda aka saba yi a kowa shekara na gasar, an karrama wasu fitatun yan wasa da suka taka rawara gani a gasar da lambobin yabo.

Ga yan wasan da kyautar da suka samu:

Gwarzon matashi a gasar bana

 

Jajirtaccen matashin dan wasan Faransa, Kylian Mbappe shine ya samu kyautar fitaccen matashi a gasar 2018.

matashin mai shekaru 19 ya taka rawar gani a gasar inda ya taimaki Faransa wajen zama zakarun bana.

kyautar dan wasa mafi kwallo

Jagoran yan wasan tawagar Ingila, Harry Kane shine ya lashe wannan kyautar bayan ya samu nasara zurra kwallaye 6 a ragar abokan adawar sa a gasar wannan shekara.

Gwarzon mai tsaron raga

 

Thibaut Courtois na kasar Belgium ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga a gasar bana. A gasar dai sau shidda kwallo ya shiga ragar shi.

Jarumin yan wasa

 

Luka Modric na kasar Croatia ya lashe wannan kayutar bayan ya taimaki tawagar kasar wajen kafa tarihi na kaiwa zagaye na karshe na gasar bana.

Fitaccen dan wasan ya nuna gwaninta da iyawa a gasar sai dai dan kwarewar shi bata kai ga nasarar lashe kofin duniya na wannan shekarar.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments