Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Ke duniya! Soja ya kashe kansa bayan ya halaka matar sa yayin da ya gano ainihin mahaifin yaran sa

Soja ya kashe matar sa kana ya kashe kansa bayan ya gano ainihin mahaifin yaran shi

Bayan binciken da yayi, ya gano cewa yaran ba nashi bane, wani abokin aikin sa ne wanda ke gaba dashi a matsayin yayi ma matar sa ciki.

Wani soja a kasar Zambia mai suna Pathias Mwape ya halaka kansa bayan ya harbe matar shin sakamakon tabbatar da cewa ba shi bane mahaifin yaran su guda biyu.

Bayan binciken da yayi, ya gano cewa yaran ba nashi bane, wani abokin aikin sa ne wanda ke gaba dashi a matsayin yayi ma matar sa ciki.

Mummanr lamarin ya faru ne a barikin sojoji inda yake zama. Kamar yadda majiya suka ruwaito, sojan ya tunkari matar sa domin tabbatar da labarin da ya jiyo daga yan anguwa.

Haduwar su ke da wuya sai ta sanar masa cewa hakika ba shi bane mahaifin yaran, abokin aikin sa ne mahaifin su.

Nan take sojan ya harbe ta da bindiga har lahira kana daga baya ya kashe kansa yayin da ya ji labari cewa yan sanda na neman sa ruwa a jallo.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments