Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Sheikh Dahiru Usman Bauchi: Bayyanar Inyass karama ce irin ta waliyyai

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ya kuma bayyana cewa su waliyyai suna iya yin abubuwan da sauran mutane ba za su iya yi ba

Sanannen  malamin addinin Musuluncin, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda shi ne "Halifan" Sheikh Ibrahim Inyass, yace bayyanar inyass a wurarre karama ce irin ta waliyyan Allah.

Ya shaida hakan ne yayin da ya zanta da BBC, kuma ya yi ikirarin cewa bayyanar Sheikh Nyass a wurin taron maulidin da aka kammala a Abuja wata karama ce" wacce Allah ya ke bai wa waliyyansa.

*Abubuwan da ya faru a maulidin Sheikh Ibrahim Inyass a garin Abuja

Wannan karin haske ne game da bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta wanda ke nuna yadda yan taro suke rububi wajen hawan fitilar haska titi domin sumbatar inda Sheikh Inyass ya bayyana.

Ya kara da cewa hakan ba wani abin mamaki ba ne domin a nuna wa mutane cewa karamar waliyyai gaskiya ce. Ya ce, "ana iya ganinsa a ko'ina. A daki ma wadansu sun sha ganinsa, ya kan bayyana haka kawai, wannan ba abin mamaki ba ne, karama ce kawai".

Jagoran mabiyan darikar tijjaniya ya kara da cewa su waliyyai suna iya yin abubuwan da sauran mutane ba za su iya yi ba.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments