Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Hukumar yan sanda: Zamu ladabtar da jami'in da ya saba ma umarnin da aka kafa - Inji Ibrahim Idris

IGP Idris orders surrender, recovery of all illegal arms in Nigeria

Ranar litinin ne hukumar ta fitar da umarni na janye ko wani jami'in hukumar dake gadin masu hannu da shuni da wasu jami'an gwamnati masu madafun iko

Babban sufeton yan sanda Ibrahim Idris yayi barazanar hukunta duk wani jami'in hukumar da ya sabawa umarni sa kan gadin wasu masu hanu da shuni da ma'aikatan gwamnati masu madafun iko.

Wannan matakin ladabtarwa ya fito bayan umarnin da ya fitar ranar litinin da ya gabata inda ya umarci da a janye duk wani jami'in hukumar dake tsaron manya masu hanu da shuni a kasar tare da jami'an tsaro.

Yayin da yake jawabi a wata taron da yayi da kwamandojin dakaru ta musamman na hukumar, baban sufeton ya sanar da matakin hukunta duk jami'in hukumar da ya saba ma umarnin da aka kafa.

"Akwai tsasauran hukumci mai jiran duk wani jami'an hukuma da ya bijire wa umarnin da aka kafa" yace.

Yace hukumar zata tsawaita kan wannan matakin da suka kafa.

A bisa bayanin shi, Idris yayi karin haske kan aikin yan sanda. Yace muhimmiyar aikin jami'an hukumar shine tabbatar da tsaro ga ko wani dan kasa.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments