Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

A Kaduna: Kotu ta dakatar da korar da gwamna yayi

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai

Game da malamai sama da 21,000 da gwamna ya kora, kotu ta daga ranar zantar da hukunci zuwa watan febreru na 2018

Kotun Ma'aikata ta kasa  dake jihar Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da korar malaman makarantun Firamare sama da dubu ashirin da gwamnatin jihar Kaduna ke aniyar yi.

Gwamnatin dai ta ce zata yi hakan bayan da malaman suka fadi jarrabawar 'yan aji hudu na Firamare wacce aka yi musu a cikin watan Oktoba.

Bisa ga faduwar su a jarabawar da aka gudanar masu gwamnatin jihar ta yanke shawarar korar su ganin cewa sun kasa tsallake jarabawar yan aji hudu na makarantar firamare.

Alkalin kotun Justice Lawal Mani ne dai ya bada umarnin dakatar da korar har sai lokacin da kotun ta duba tare da yanke tabbatacce hukunci a bisa wannan kara.

Kotun dai dage sauraren karar har zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2018.

Game da batun korar gwamnan jihar Malam Nasiru El-rufai yace za'a sauya malaman da wasu 25,000 wadanda suka cancanta bayan an gudanar da zaman zantawa.

Sakamakon korar ya sanya kungiyar malamai da ta yan kwadudo na jihar suka gudanar da zanga-zanga na tsawon kwanaki da dama. Cikin wuraren da suka kai koken su har ma rahoto ya nuna cewa sun barnata dukiyoyi akwai gidan majalisar dokoki na jihar.

Karanta labarin>> Gwamna ya biyo sahun gwamnatin jihar Kaduna wajen tantance malamai

Labarin dai yayi tada kura a fadin kasa inda jama'a da dama sunyi tsokaci game da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka a matsayin wanda ya dace. Shima shugaba Muhammadu Buhari ya goyi bayan gwamna  jihar inda yake cewa idan har ba'a samu ingantaccen malamai toh lalle fannin ilimi zata fuskanta kalubale.

Hakazalika wasu da dama na ganin cewa hukuncin yayi tsauri ganin yawan malaman da hukuncin ya shafa.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments