Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Lai Muhammed: Farashin shinkafa zai sauka nan bada jimawa ba - inji minista

Buhunan shinkafa

Yayin da yake ganawa da yan jarida ranar laraba a garin Abuja ministan yace shinkafa ya kasance nau'in abinci wanda aka fi ci a kasar.

Ministan labarai da al'adun gargajiya alhaji Lai Muhammed ya tabbatar ma yan Nijeriya cewa gwamnatin shugaba Buhari tana iya bakin kokari ta wajen ganin farashin shinkafa ya sauka.

Yayin da yake ganawa da yan jarida ranar laraba a garin Abuja ministan yace shinkafa ya kasance nau'in abinci wanda aka fi ci a kasar.

Ministan yace gwamnatin tarayya ta dau matakin wajen rage yawan shigowa da shinkasa kasar daga kasashen waje ta hanyar inganta harkar noman shikafa tare da karfafa gwiwan masu noman ta.

 

Lai Muhammed ya kara da cewa shigowa da ake yi da shinkafa daga kasar thailand ya ragu sosai domin a cikin shekara 2015 ana shigowa da kimanin tan 644,131 amma a cikin 2017 an samu shigo da tan 21,000.

Wannan sanarwan ya fito bayan wanda labarin da ya fito a baya inda Manoman shinkafa suka ce za'a rage farashin ta zuwa 6000

Ministan yace gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na bakin kokarinta wajen samad da tan 7,000,000 cikin shekara 2018.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments