Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

El-Rufai: Gwamna ya sallami ma'aikata sama da 4000 na kananan hukumomi

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai

A bisa takardar da gwamnatin jihar ta fitar ma manema labarai, gwamnan yace wannan matakin zata taimaka wajen rage ma'aikata a kananan hukumomin zuwa yanda ya kamata.

Gwamnan jihar Kaduna malam Nasir Elrufai ya sannu ga takarda gake bada umarni na rage ma'aikatan kananan hukumomi na jihar zuwa 7000 tare da sallamar mutum 4000.

A bisa takardar da gwamnatin jihar ta fitar ma manema labarai, gwamnan yace wannan matakin zata taimaka wajen rage ma'aikata a kananan hukumomin zuwa yanda ya kamata.

Shi dai gwamnan yace wannan sabon umarni ba shafi malamai dake karkashin hukumar SUBEB na jihar da kuma ma'aikatan cibiyar kiwon lafiya.

Gwamna yana mai cewa;

 "Babban dalilin da ya sanya kananan hukumomi na fama da rashin kudi shine domin suna da ma'aikata fiye da ki'ima.

Batun yawan ma'aikata shine dalilin da ya sanya kananan hukumomi basu iya biyan albashin ma'aikatan su ba tare da sun nemi taimakon gwamnatin jiha.

Da haka, muka fitar da adadin ma'aikatan da ya kamata a samu a duk kananan hukummin 23 dake jihar. Mun rage yawan ma'aikatan zuwa 7000 a jimlace."

Wannan matakin bai shafi malaman hukumar SUBEB da ma'aikatan cibiyoyin kiwon lafiya.

"Na sa hannu ga takarda dake neman goyon bayan masu ruwa da tsaki na kananan hukumomin 23 muke dashi a jihar kan adadin ma'aikata da ya kamata a samu."  yace.

Karanta labarin>> Tsokacin da gwamna yayi game da ficewar Atiku daga Jam'iyar APC

Wannan sabon matakin ya fito bayan sallamar malamai 21,780 da gwamnan yayi faduwar su a jarabawan da aka gudanar masu musamman domin tantance masu ilimi a cikin su wanda ya tada kura a fadin kasar.

Sakamakon hakan ne kungiyar malamai da na yan kwadago na jihar sun nuna facin ran su game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka tare da yin zanga-zanga a jihar domin nuna fushin su.

Duk da zanga-zanga da kungiyoyin suka yi gwamnan ya jajirce akan bakan shi na sallamar su sai dai ya bai wasu daga cikin su damar kara neman aiki cikin sabbin maikata da za'a dauka indai sun san zasu ci jarabawan da za'a kara yi ni na tantance sabbin mallamai 25,000 da za'a dauka.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments