Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Atiku Abubakar: Tsohon Mataimakin shugaban kasa ya sauya sheka daga jam'iyar APC

Atiku Abubakar

Atiku yace jam'iyar APC bata cinma burin ta ba kuma tana dab da samun cikas

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sauya sheka daga jam'iyar APC.

Atiku yayi murabus daga jam'iyar APC yace jam'iyar  bata cinma burin ta ba kuma tana dab da samun cikas

A wata takarda da ya sa hannu ranar juma'a 24 ga watan nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasa wanda ya kasance tamkar jigo a jam'iyar APC ya nuna bacin ran sa ga yanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bata jawo matasa  ba cikin tawagar sa.

karanta Yan Nijeriya baza su sake zaben PDP - inji jam'iyar APC

Atiku yayi iki'rari cewa jam'iyar APC bata biya bukatun jama'a da suka yi alkawarin biya kuma bata neman membobin jam'iyar domin neman shawara ko kafin ta aikata ayyukan ta.

Wannan sabon al'amarin ya faru bayan wata bidiyo da tayi yawo a duniyar gizo inda Tsohon mataimakin shugaban kasa ke bayyana anniyar sa na zaben 2019

Atiku Abubakar ya sauya sheka zuwa jam'iyar APC cikin watan febreru na 2014 daga jam'iyar adawa ta PDP inda ya samu damar zama mataimakin shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.

A bisa takardar da ya fitar tsohon mataimakin shugaban kasa yace bayan ya nemi shawarar daga Allah da iyalen sa da magoya bayan sa ya yanke hukunci yin murabus daga jam'iyar APC kana zai yi nazari kafin ya sanar da sabuwar akidar sa.

 

 



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments