Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Tura ta kai bango: Magidanci ya kashe uwardakin sa bayan ya kama ta da aikata zina

Bello Muhe ya kashe matar sa kan zargin aikata fasikanci

Bello Muhe ya kashe matar sa Husse Ali bayan tayi kunnen kashi da umarnin da ya bata na daina fasikanci.A

Wani magidanci a jihar Niger mai suna Bello Muhe ya kashe uwardakin sa bayan ya zargi ta da yin zina.

Magidancin ya kashe matar sa Husse Ali mai shekara 25 bayan da ya bayyana cewa tayi kaurin suna wajen aikata fasikanci duk da gargadin da ya bata na daina hakan.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana Bello Muhe wanda asali dan karamar hukumar Bagudu ne na jihar Kebbi, ya tura matar sa gidan iyayen ta bayan ya kamata da aikata fasikanci da wani. Ta cigaba da aikata mummunar aikin bayan komawa gidan iyayen ta.

Labari ya bayyana cewa bayan roko da jama'a suka yi masa na ya dawo da ita gidan sa. Amma duk da dawowar ta ta cigaba da aikata abun takaicin.

Bello ya zantar ma jaridar Northern city news yadda ya kashe matar tasa kamar haka:

"Na tsare ta da adda bayan ta bijire ma umarnin da na bata. Ya bata umarni na daina aikata fasikanci da mazaje amma ta ki kuma bisa ga haka na fusata har na kashe ta. Tayi kunnen kashi da gargadin da nayi mata don haka ta gamu da wannan mummunar sakamako".

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Niger, Muhammed Abubakar, ya tabbatar da faruwar haka kana ya kara da cewa ana cigaba da bincike kan lamarin kuma bayan haka za'a gurfanar dashi gaban kotu.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments