Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Labarin Kannywood: Sani Danja yayi murnar cika shekara 11 aurensa da Mansura Isa

Sani Danja tare da matar sa Mansura Isa

Fitaccen jarumin yayi murnar cika shekara sha daya auren sa da tsohuwar jarumar fim, mansura Isa.

Fitaccen jarumin masana'antar fim ta Kannywood kuma tauraro a masana'antar Nollywood, Sani Musa Danja yayi murnar cika shekara 11 da aure.

Jarumin ya raya ranar auren sa da matar sa kuma tsohuwar jarumar fina-finan hausa, Mansura Isa.

Ma'auratan sunyi murnar zagayowar wannan ranar ranar hutun kashen makon da ya shude.

Jigo a masana'antar Kannywood yayi farin cikin zagayowar wannan ranar a shafin sa na kafar sada zumunta. Ya wallafa hoton shi tare da uwardakin sa tare da rubuta sako mai narkar da zuciya.

 

Auren su wanda aka daura cikin watan Yuli na shekarar 2007 sun samu albarkacin yara hudu, mace daya da maza uku.

Dalilin barin masana'antar Kannywood

Mansura Isa tana daya daga cikin tsofafin jarumai yan fim da suka nishadantar da al'umma shekarun baya. tauraron ta ya haska matuka.

Sai dai bayan aurenta aka daina jin duriyar ta a farfajiyar fim.

Hirar ta da Premiumtimes kwanan baya, jarumar ta bayyana cewa duk wani nasara da take bukata a rayuwa ta samu yayin da take yin fim.

Mansura tace ta daina fitowa a fim bayan tayi aure domin ta kula iyalinta da gidan su.

"Hakika na daina damawa a harkar nishadantarwa tunda nayi aure domin in kula da gida na da iyalina. Allah ya bani sa'a da na samu miji nagari wanda ke kaunata kuma muna taimakon juna wajen inganta auren mu. Abun kamar mafarki, kusan shekara 12 kenan da auren mu kuma muna da yara hudu wannan abun farin ciki ne sosai" tace.

Da take bada amsar tambayar da aka yi mata na cewa ko tana kewar fitowa a fina-finai tace;

"Gaskiya bana kewar yin fim domin na samu nasara na kololo kafin na bar kannywood domin sanadiyar fim na gina gida na kaina, na siya mota, na tafi aikin hajj bugu da kari na auri gwarzon kannywood. Babu abun da zan iya cewa sai dai inyi ma Allah godiya".

Tsohuwar jarumar ta kasance mace ta farko da ta fara aikin edita a masana'antar kannywood.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments