Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Aminu Tambuwal: Mace ta farko da ta zama farfesa a jihar Sokoto ta samu sabon mukami

Farfesa Aisha Madawaki tare da sauran sabbin kwamishnoni a bikin rantsarwa

Farfesa Aisha Madawaki malama ce a fannin ilimin halayen dan adam a nan jami'ar Usman Danfodio dake jihar Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya rantsar da mace ta farko da ta zama farfesa a fadin jihar a matsayin kwamishna tare da wasu.

Farfesa Aisha Madawaki malama ce a fannin ilimin halayen dan adam a nan jami'ar Usman Danfodio dake jihar.

An rantsar da ita a matsayin kwamishnar ilimi tare da Ahmed Barade Wamakko da Garba Yakubu Tsitse da Bello Isa Ambarura a matsayin kwamishnoni ranar talata 16 ga watan janairu 2018.

 

Duk a cikin sabon rantsarwa da gwamnan yayi akwai tsohon dan majalisar wakilai Umar Bature da tsohon shugaban makarantar kimiya ta jihar dakta Bello Rabiu Alkali wadanda aka nada a matsayin masu baiwa gwamnan shawara akan ayyuka ta musamman tare da Alhaji Bello Buba wanda aka ratsar a matsayin sabon shugaban karamar hukumar Wamakko.

A jawabin shi a bikin rantsuwa da aka gudanar a gidan gwamnati jihar, gwamna Tambuwal ya shawarci sabbin kwamishnonin da su amfani da wannan damar wajen biyan bukatar al'ummar jihar da samad da cigaba a jihar.

Tambuwal yace gwamnatin shi na kan tafarkin inganta rayuwar al'ummar jihar ta hanyar aiwatar da ayyukan cigaba.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments