Monday, 17 July 2017

Shehu Sani: Sanata yayi wa T.Y Danjuma kashedi na ya kama bakin shi

Senator Shehu Sani (right)

Sanata Sani yayi Allah-wadai game da tsokacin da dattijon ya bayar inda yace irin su ke haifar da tashin hankali a kasar.

Sanatan mai wakiltar arewacin jihar Kaduna ya yi wa T.Y Danjuma kashedi na ya kama bakin shi akan kalamu masu haifar da tashin hankali.

A baya Danjuma da wasu yan ƙungiyar dattawan adinin kristoci na kasa (NCEF) sun zargi shugabancin Buhari da kawo rikicin kabilanci tare da zuga rarrabuwa tsakanin ‘yan kasar.

A bisa labarin Daily post Sani ya yi watsi da tsokacin inda yace ire-iren wadannan kalamun ke yi wa ƙyakkyawar zamantakewar yan kasar barazana

Yana cewa “ rashin adalci ne idan wani ko wasu na zargin shugaba Buhari ko shugabancin shi da wata manufa dangane da addini. Sauran batutuwa da ake tsokaci akan su game da shi ko shugabancin shi suna iya kasance gaskiya amma indai maganar addini ne shi ba mai tsannanta bane. In dai akwai wani shaida akan manufar wanda ya danganci addini ni zan fara busa kaho.”

“Dattawa su kasance masu haifar da zaman lafiya da hadin kan yan kasa ba su kasance masu wura wutar rikici. A wannan lokacin da kasar ke ciki bamu son tsegumi da zai haifar da rikicin kabilanci ko na addini”

“Batun addini ko kabilanci yana iya lalata zamantakewar mu a matsayin yan kasa. Dole mu hada kai wajen magance duk wani batu da zai zuga ‘yan kasa indai kan addini ne ko na kabilanci”

Wannan ya fito dai dai lokacin da ƙungiyar matasan arewa ke zargin wasu shugabannin siyasa na yankin gabashin kasar da makircin cire shugaba Buhari daga mukamin shi.from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

No comments:

Post a Comment

Feel free to drop your comments to help us serve you better