Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Osinbajo: Gwamnatin tarayya zata gina gidaje 3000 ma yan gudun hijira dake Bama

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Mukaddashin shugaban ƙasa yace tsarin zai yi sanadiyar gina gidaje, ofishoshin yan sanda, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya

Gwamanatin tarayya na shirin gudanar da gine-gine don taimakawa wadanda riĆ™icin yan ta’adda ya shafa a yankin arewa maso gabas na Ć™asar karkashin wani tsari da ta kirkiro mai taken ‘Bama initiative scheme’.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka a wani takarda da kakakin sa mista Laolu Akande ya fitar.

Akande ya zayyana cewa mukaddashin shugaban kasa ya gana da gwamna jihar Borno Kashim Shetima, wasu ministoci tare da wasu shugabanin ma'aikata a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar litinin.

Osinbajo ya bayyana cewa tsarin zai kai ga gina gidaje 3000, ofishin yan sanda 10, makaranta firamari da sakendari 18, cibiyoyin kiwon lafiya da kafa jami’an tsaro na musamman tare da samad wa mafaurata 1500 aiki.

Osinbajo yana cewa; “A cikin tsarin Bama initiative gwamnatin tarayya zata bada kaso 67 na tallafi kuma gwamnatin jihar Borno zata cika sauran kaso 33”

“Babu shakka wannan tsarin zai taimaka

Cikin wannan tsarin garuruwa kamar Bama, Banki, Gulumba gara da dai sauran su zasu ci moriyar ayyukan da za’a gudanar.

Ana sa ran cewa za’a aiwatar da tsarin cikin ‘yan makonni da zai gabata.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments