Monday, 17 July 2017

Obasanjo: Duk wanda ya kira ni da suna Mathew zai sansana kashin shi - inji Obasanjo

Former Nigeria president, Olusegun Obasanjo.

Tsohon shugaban kasa nanata cewa baya son ana kiran shi da sunan wanda a cikin littafi mai tsarki na kristoci yana nufin mai karban haraji

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wa wadanda ke neman kiransa da sunan addini gargadi na kada su kuskura yin haka ko kuma su hadu da fushin shi.

A rahoton da Vanguard News ta fitar, tsohon shagaban kasa yayi wannan bayani a bikin cika shekara 80 a duniya.

Yace ya cire sunan Mathew daga sunayen shi don a littafi mai tsarki na kiristoci yana nufin ‘mai karban haraji.

Yana cewa “Iyaye na suka samun sunan lokacin da suka haifeni kuma na taso ana kira na da sunan.

Menene ma’anar sunan? Mai karban haraji.”

“Da na mallaki hankali sai na tsoke Mathew daga sunaye na. Indai mutum baya son ya hadu da fushi to kada ya kuskara ya kira ni da haka.”

Obasanjo yana daya daga cikin shugabannin da tsarin mulkin su na nuna jajircewa kuma ya magance kusan duk wani ƙalubale da kasar ke fuskanta a zamanin mulkin shi.

Har wayau akwai wasu ‘yan kasar dake ganin cewa inda shine a kan kujerar mulki yanzu da ya kawo karshen ƙungiyar boko haram dake takura ma yankin arewa maso gabas.from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

No comments:

Post a Comment

Feel free to drop your comments to help us serve you better