Monday, 17 July 2017

Ibrahim Magu: Fadar shugaban kasa tace bata bukatar tabbacin ‘yan majalisa dangane da shugaban huƙumar EFCC

Acting Chairman of the EFCC, Ibrahim Magu

Wannan ya fito bayan shawarwarin da masana kan fannin shari’a suka bada inda suka yin la’akari da sashi 171 na ƙundun tsarin mulkin na ta 1999

Fadar shugaban kasa ta saya a kan batun ta na cewa Ibrahim Magu suka nada a matsayin shugaban huƙumar yaki da rashawa kuma ba ta bukatar tabbacin ‘yan majalisa

Fadar shugaban kasa ta dogara da shawarar da masana akan fannin shari’a suka fitar na sashi 171 cikin ƙundun tsarin mulkin kasa

A labarin da jaridar the Nation ta fitar, lauyoyin sun bada shawarar yayin da suka yi la’akari da dokar da mai shari’a Walter Onnoghen ya zartar kafin ya samu matsayin da yake yanzu

Mai shari’a Onnoghen ya zartar da doka inda ya dora da cewa ƙundun tsarin mulkin kasa na gaba da ko wani tsarin doka.

Fadar shugaba tace dai zata jira sharhin masu shari’a game da sashi 171 don gano makomar Ibrahim Magu.

Masanan sun kara da cewa shugaban kasa na da ikon nada ko wani mutum a matsayin mukaddashi a mukamin shugabancin huƙumar EFCC.

Sunyi misali da mubaya’an marigayi Abraham Babalola Borishade da Shugaba Olusegun Obasanjo yayi wanda ‘yan majalisa suka yi watsi dashi har sau hudu cikin wata 18 amma a karshe sun tabbatar da nadin sa a matsayin minista.from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

No comments:

Post a Comment

Feel free to drop your comments to help us serve you better