Monday, 17 July 2017

A garin maiduguri: Mutum 10 sun rasu sanadiyar farmaki da yan kunar bakin wake suka kai a masallaci

10 reported dead as suicide bombers attack Maiduguri mosque

‘Yan kunar bakin wake sun tada bam a cikin masallaci yayin da ake sallar asuba

Mun samu labari cewa akalla mutum 10 suka mutu yayin da yan kunar bakin wake suka kai hari a masallacin jami’ar Maiduguri asubancin ranar litinin 17 ga watan Yuli.

Har yanzu dai babu wata karin bayani game da harin amma bisa ga labarin Daily trust yan ta’adar sun tada bam a masallacin yayin da ake sallar asuba.

Jaridar sun ta kawo rahoto cewa mace ce ta kai harin.

Daily mail tace bam din ya fashe dai-dai karfe 5:30 a unguwar London ciki dake garin Maiduguri.

Mun kara samun labari cewa an kai farmaki a wurare da dama a cikin babban birnin jihar Bornofrom pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

No comments:

Post a Comment

Feel free to drop your comments to help us serve you better